in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Barca tana goyon bayan Messi a shari'ar da yake fuskanta
2016-07-12 15:56:09 cri

Kulob din Barcelona ya kaddamar da aiki mai taken 'We Are All Leo Messi' ma'anar 'dukkan mu Leo Messi ne' don nuna goyon baya ga dan wasanta dan asalin kasar Argentina, wanda ke fuskantar hukunci da aka yanke masa sakamakon zargin da ake masa na yin magudi wajen kin biyan kudaden haraji.

Dan wasan mai shekaru 29 a duniya, da babansa, suna fuskantar hukuncin daurin watanni 21 a gidan kaso, kana aka ci tararsu har Euro miliyan 2, bayan da aka zargesu da cutar hukumar karbar haraji ta kasar Spainiya da kudin Euro miliyan 4.1 tsakanin shekarun 2007 da 2009.

A nasu bangaren, Messi da babansa sun tsai da niyyar kin karbar hukuncin da aka yanke musu, haka kuma sun ce za su daukaka kara don a wanke su daga zargin da aka yi musu.

Ganin haka ya sa kungiyar Barcelona ta yi kira ga masu goyon bayanta da su mu su marawa dan wasan kasar Argentinan baya, ta hanyar halartar gangamin da kungiyar ta kaddamar na 'We Are All Leo Messi'.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China