Kakakin ma'aikatar tsaro ta Sin Yang Yujun ya yi jawabi kan manufofin tsaro na kasar Sin a gun taron manema labaru a jiya Alhamis, inda aka dora muhimmanci sosai kan batun tekun kudancin Sin. Mr. Yang ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta taba tada rikici ko haifar da sabani a kan batun tekun kudancin Sin ba, matakan da Sin ta dauka sun dace da doka, kuma ta iya daukar nauyin dukkan ayyukan da ta yi. Amma idan wasu kasashen waje sun tada rikici a wannan yanki bisa fakewa da shimfida zaman lafiya, to ko shakka babu kasar Sin za ta mayar da martani kansu.
Mr. Yang ya nanata cewa, "kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan kiyaye mulkin kai da kuma ikonta a yankin teku, za ta kiyaye zaman lafiya a tekun kudancin Sin ba tare da kasala ba, kana za ta ci gaba da yin shawarwari tare da kasashen da abin ya shafa bisa tarihi da dokar duniya domin daidaita batun cikin ruwan sanyi. A sa'i daya kuma, rundunar soja ta Sin tana da niyyar kiyaye mulkin kai da kuma cikakken yankin kasa."
A cikin dogon lokaci, kasar Amurka da wasu sauran kasashen waje sun gudanar da aikin soja a wannan yanki, bisa fakewa da kiyaye zaman lafiya. A game da haka, Yang Yujun ya zargi su sosai. Ya ce, wadannan kasashe sun tsoma baki kan harkokin tekun kudancin Sin ne sabo da neman moriyarsu, abin da suka yi ya kawo cikas ga shimfida zaman lafiya a yankin. Yayin da Mr. Yang ke magana kan zirga-zirgar wasu jiragen ruwan soja na kasar Amurka a wannan yankin, ya bayyana cewa, ba za a iya tabbatar da zaman lafiya a yankin tekun kudancin Sin ba, sai dai bayan jiragen ruwan soja na kasar Amurka sun daina nuna karfinsu a yankin.(Lami)