Mr. Deby, shugaban kwamitin CILSS a wannan karon, ya ce, ya kamata mambobi kasashen kwamitin su dukufa wajen daidaita saurin karuwar jama'a da na rasuwar al'umma cikin kasashensu, ya kuma yi kira ga mambobi kasashen da su dauki matakai yadda ya kamata domin daidaita saurin karuwar jama'a, raya tattalin arziki da kuma samar da karin guraben aikin yi. Ya kara da cewa, idan ba za a iya warware matsalar saurin karuwar jama'a a yankin Sahel ba, batun zai haifar da illa ga samun isashen abinci, aikin yaki da bala'in fari da kuma hana ci gaban hamada a yankin. (Maryam)