in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci a kawo karshen rikicin kasar Sudan ta Kudu
2016-07-11 11:12:26 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa jiya Lahadi, inda ya nuna matukar mamaki kan rikicin da ya abku a tsakanin bangarorin sojojin kasar Sudan ta Kudu a Juba babban birnin kasar, kuma ya kalubalanci shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar, da su yi iyakar kokarinsu wajen kawo karshen nuna kiyayya a junansu, don kawo karshen rikicin da kuma maido da zaman lafiya a kasar.

A wannan rana kuma, ofishin kakakin MDD ya bayyanawa kafofin watsa labaru cewar, kwamitin sulhu na MDD ya tsai da kudurin kiran taron gaggawa domin tattaunawa kan halin da kasar Sudan ta Kudu ke ciki.

A ranar 9 ga wata, kwamitin sulhu ya bayar da sanarwa, inda ya yi Allah wadai game da barkewar sabon rikicin, kuma ya bukaci gwamnatin wucin gadi ta sulhuntar al'ummar kasar da ta bi bahasin lamarin da kuma daukar matakai don kawo karshensa, a kokarin sassauta hali mai tsanani da ake ciki a kasar.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China