in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Red Cross ta kwashe mutane 17 da suka samu raunuka yayin rikici a Sudan ta Kudu
2016-06-20 11:02:04 cri
Kwamitin hukumar bada agajin ta Red Cross (ICRC) ya fada cewar ya kwashe mutane kimanin 17 ta hanyar amfani da jiragen sama daga garin Raja na kasar Sudan ta Kudu, bayan barkewar wani tashin hankali da yayi sanadiyyar rayukan mutane masu yawa.

Shugaban tagawar ta ICRC a Sudan ta kudu Juerg Eglin ya fada cewar hukumar bada agajin ta kasa da kasa ta tura jiragen sama biyu da tawagar jami'an kiwon lafiya zuwa garin Raja domin kwashe mutanen da suka samu munanan raunuka.

Cikin wata sanarwa daya fitar a Juba Eglin, ya bukaci dukkan bangarorin da basa ga maciji da juna su fahimci cewar ya kamata su magance cutar da fararen hula, kuma su basu damar halartar cibiyoyin kiwon lafiya da aka tanada.

A ranar Larabar data gabata ne, wasu mahara dauke da makamai a Sudan ta kudu suka hallaka wasu sojojin gwamnatin kasar a yayin da suka yi yunkurin kaddamar da hari kan jami'an gwamnatin a garin Raja.

Harin na safiyar ranar Laraba, yayi sanadiyyar tilasta daruruwan jama'a ficewa daga gidajensu domin neman mafaka.

Bayan barkewar tashin hankalin an sace 3 daga cikin motocin hukumar ta Red Cross.

Sai dai har ya zuwa yanzu, babu wata kungiya data dauki alhakin kaddamar da harin, sannan gwamnatin kasar bata samu nasarar damke wadanda suka jagoranci kaddamar da harin ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China