in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna damuwa kan cigaban rikici a Juban Sudan ta Kudu
2016-07-09 11:55:52 cri
Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya bayyana a ranar Jumma'a damuwa sosai game da cigaban tashe tashen hankali a Juba, da kuma yadda yake ganinsu a matsayin wani rashin kulawa ta bangarorin da abin ya shafa dangane da shirin zaman lafiya.

Ya ce yana matukar damuwa kan barkewar rikici a Juba tsakanin rundunar sojojin Sudan ta Kudu (APLS) da dakarun APLS dake adawa. Barkewar rikicin a babban birnin kasar, a jajibirin cikon shekaru biyar da samun 'yancin kasar, ya kasance wani abin da ke nuna rashin kulawa game da alkawarin bangarorin wajen tabbatar da shirin zaman lafiya, wanda kuma ya zama wani cin amana ga al'ummar Sudan ta Kudu dake cigaba da shan munanan wahalhalu da bai kamata a amince da su ba tun cikin watan Disamban shekarar 2013, in ji sakatare janar na MDD a cikin wata sanarwa.

Ya ce yana nuna damuwa sosai game da barkewar tashin hankali a Wau da Bentiu, wanda zai kai ga lalata yanayin tsaro a dukkan fadin kasar. Yana kuma kiran da a girmama 'yancin jin kai na kasa da kasa bisa tanadin MDD, da kuma baiwa abokan huldarsu damar kai taimako ga mutanen dake cikin bukata, in ji mista Ban.

Haka kuma, yayi kiran gaggawa ga shugaba Salva Kiir da mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar dasu yi kokarin kawo karshen tashen tashen hankalin dake cigaba, tare da ladabtar da shugabannin sojoji game da tashe tashen hankali, kana dasu yi aiki tare da abokan hulda domin aiwatar da yarjejeniyar warware rikicin kasar Sudan ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China