in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Equatorial Guinea ta goyi bayan daidaita batun tekun kudancin Sin ta hanyar yin shawarwari
2016-07-08 13:02:50 cri
Babban sakataren jam'iyyar tabbatar da tsarin dimokuradiyya a Equatorial Guinea Jeronimo Osa Osa Ecoro ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ya kamata kasashen da batun tekun kudancin Sin ya shafa su yi shawarwari bisa Kundin Tsarin MDD da dokar duniya, domin daidaita batun cikin ruwan sanyi.

A yayin da Jeronimo Osa Osa Ecoro ke zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar Philippines ta gabatar da karar yanke hukunci kan batun tekun kudancin Sin bisa kashin kanta, lallai wani lamari ne da bai dace ba, kana wannan matakin da ta dauka zai kawo cikas ga shimfida zaman lafiya a yankin. A madadin jam'iyyarsa, Jeronimo Osa Osa Ecoro ya yi kira ga kasar Philippines da ta yi shawarwari tare da Sin wajen daidaita batun ta hanyar siyasa, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China