Rahoton ya ce, ya zuwa ranar 12 ga watan Mayu, kimanin mutanen Sudan ta Kudu dubu 69 sun shiga kasar Sudan ta yankin arewacin iyakar kasa, a ciki kimanin mutane dubu 46 sun isa jihar East Darfur. Rikice-rikice, da karancin amfanin gona, da raguwar darajar kudi, da kuma hauhawar farashin abinci, sun janyo ficewar mutane da dama daga Sudan ta kudu
A ranar 17 ga watan Maris na bana, gwamnatin Sudan ta yanke shawarar kebe mutanen Sudan ta Kudu dake zama a Sudan a matsayin 'mutanen ketare', wadanda za su yi zama a Sudan kamar yadda sauran kasashen waje suke. Kuma za a dauki matakai bisa doka kan duk mutanen Sudan ta Kudu da suka shiga kasar Sudan ba tare da takardar izini ba.(Fatima)