in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Sulhu na MDD ya sake maida takunkumi kan kasar Sudan ta Kudu
2016-06-01 10:44:17 cri
A ranar Talata, kwamitin sulhu na MDD ya sake maida takunkumi kan kasar Sudan ta Kudu na karin shekara guda bisa yunkurin tallafawa aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a cikin kasar.

Bisa wannan kuduri da aka cimma bisa babban rinjaye, kasashe mambobi na kwamitin sun dauki niyyar sake maida haramcin tafiya tafiya da rike kudade ga mutanen dake kasancewa tarnaki ga yarjejeniyar zaman lafiya tare da kara wa'adin gungun kwararru dake sanya ido kan takunkumin bisa tsawon watanni 13.

Kwamitin ya kuma bayyana damuwarsa game da rikicin dake tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da dakaru masu adawa wanda ya barke daga sabanin siyasa na cikin gida.

Tashe tashen hankali sun barke a cikin wannan kasa mai arzikin man fetur kana jinjirar kasa a duniya shekaru biyu bayan ta samun 'yancin kai, a shekarar 2011, a lokacin da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya zargi shugaban 'yan tawaye, Riek Machar da yunkurin shirya juyin mulki.

Yarjejeniyar daidaita rikici a kasar Sudan ta Kudu da aka sanya hannu a ranar 17 ga watan Augustan shekarar 2015 ta taimaka wajen kawo karshen yakin basasa na watanni 21 wanda ya salwantar da rayukan dubun dubatar mutane da kuma janyo hijirar wasu miliyoyin jama'a.

A karshen watan da ya gabata, Sudan ta Kudu ta kafa gwamnatin hadaka ta wucin gadi, da kwamitin sulhu ya nuna yabo a matsayin wani muhimmin mataki wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China