Sudan ta Kudu: Gwamnatin hadin kan 'yan kasa na fuskantar barazana daga mayakan sa kai
Kwararru na ganin cewa gwamnatin hadin kan 'yan kasa, da aka kafa a karshen watan Afrilu, dole ne ta mai da hankali da farko wajen kawo sauyi ga harkokin tsaro da sake daidaita tattalin arzikin kasar dake da rauni domin kaucewa wannan sabuwar kasa sake fadawa cikin yakin basasa. Sabuwar gwamnatin Sudan ta Kudu na fuskantar wani babban kalubale da ya shafi sake gina abubuwan more rayuwar jama'a da aka lalata da kuma biyan albashi na wani adadin yawan ma'aikata. Ma'aikata da dama ba su samu albashinsu ba tun yau da watanni biyu, har ma da sojoji da 'yan sanda, tsofin mambobin kungiyar 'yan tawayen kwato 'yancin al'ummar Sudan dake adawa (SPLM-IO) dake karkashin jagorancin maitaimakin shugaban kasa Riek Machar. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku