Jakadan kasar Sin a Sudan ta kudun Ma Qiang, shine ya tabbatar da hakan a Juma'ar data gabata, yace tallafin zai taimaka wajen kudurin da shugaba Salva Kiir da mataimakinsa na farko Riek Machar suka dauka na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da nufin kawo karshen yakin basasar da ya daidaita kasar shekaru 2 da suka gabata.
Jakadan na Sin ya kara da cewar, wannan tallafin ya nuna a fili yadda gwamnatin kasar Sin ke bada muhimminmanci game da samar da dawwamamman zaman lafiya a Sudan ta kudu.
Shi dai mista Machar, shine madugun 'yan tawayen SPLM-IO wadanda ke yaki da gwamnatin kasar, kuma a ranar Talatar data gabata ne ya koma Juba inda aka rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban kasar ta Sudan ta Kudu, wannan mataki na daga cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a watan Augastan shekarar bara tsakanin bangarorin biyu karskashin jagorancin MDD.
A wani cigaban kuma, an rantsar da sabbin ministocin da aka zaba na gwamnatin rikon kwarya ta hadin kan kasa a ranar Juma'ar da ta gabata.(Ahmad)