Majalisar ta amince da wannan mataki ne a lokacin taronta wanda ta gudanar a ranar Talatar da ta gabata.
A yayin gabatar da kudurin wanda ya samu amincewar mambobin MDD na kasashen duniya 193, taron ya dauki wannan mataki ne bisa abin da ya ambata cewar kasashen duniyar masu zafi na taka muhimmiyar rawa wajen samar da cigaban duniya, amma duk haka suna fuskantar kalubale mai tarin yawa wanda yake bukatar duniya ta maida hankali kansa domin cimman nasarar samun dauwwammen cigaba.
MDD ta lura cewar, kasashen masu zafi su ne kaso 40 cikin 100 na fadin kasa da ake da shi a duniya baki daya, har ila yau, kasashen su ne ke da kaso 80 cikin 100 na muhallin hallitu da ake da su a fadin duniya, sannan baya ga irin harsuna da kabilu masu yawa da kasashen ke da su.
MDD ta gayyaci dukkan mambobin kasashen duniya, da hukumomin MDD, da kungiyoyin kasa da kasa da kungiyoyin al'umma ciki har da hukumomi masu zaman kansu, da su gudanar da bikin tunawa da wannan rana kamar yadda ya kamata, domin gabatar da muhimman batutuwa da suka shafi kalubale dake addabar kasashen masu zafi da hanyoyin magance su. (Ahmad Fagam)