A yayin bikin rantsuwar kama aikin, mista Machar ya bayyana cewa, tabbatar da tsaro da zaman karko da kuma raya tattalin arziki muhimmin aiki ne a gaban kasar Sudan ta Kudu.
Shugaban kasar ta Sudan ta Kudu Salva Kiir ya yi maraba da komowar Machar a yayin bikin, a ganinsa komowarsa a Juba ya nuna cewa, an kawo karshen rikici a cikin kasar, kuma kafa gwamnatin wucin gadi ta hadin kai hanya ce daya kacal da ake bi wajen kawo karshen rikici, da farfado da zaman lafiya da zaman karko a kasar.
A jiya kuma babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa ta yawun kakakinsa, inda ya yi maraba da komawar Machar Juba, da kuma kama aikinsa a matsayin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu, ya kuma yi kira ga kasar da ta kafa gwamnatin wucin gadi ta hadin kai cikin sauri.
A wannan rana kuma, kwamitin sulhu na MDD ya kira taro game da yanayin da Sudan ta Kudu ke ciki, inda mataimakin babban sakataren kungiyar mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Hervé Ladsous ya ce, muhimman matakai biyu da kasar za ta dauka a nan gaba su ne, kafa gwamnatin wucin gadi ta hadaka, da gudanar da ayyukan tsaro a yayin mulkin wucin gadi. (Bilkisu)