in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukuncin da za a yanke kan batun tekun kudancin Sin ya sabawa dokar kasa da kasa
2016-07-06 14:47:08 cri
Kwanan baya, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin ya yi sharhi cewa, hukuncin da za a yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin bisa rokon kasar Philippines kadai shi ya sabawa doka, lamarin ne tamkar wani wasan siyasa. Kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye ikonta kan yankin tekun kudancin kasar bisa dogaro da tushen tarihi da dokoki yadda ya kamata, da kuma ya dace da yarjejeniyar teku ta MDD, kana, hukuncin da za a yanke kan tekun kudancin kasar bisa rokon kasar Philippines kadai bai dace da dokokin kasa da kasa ba, dalilin haka ne, kasar Sin ba za ta amince da wannan hukuncin da za a yanke ba.

Haka kuma, cikin wannan sharhi, Mr.Liu ya ce, kotun yanke hukunci ta yi musu kan aniyar kasar Sin da kasar Philippines kan warware sabaninsu ta hanyar sulhu, ta kuma yi musu kan sanarwar da kasar Sin ta fidda bisa yarjejeniyar teku ta MDD, sai ta gudanar da bincike kan batun da kanta, lamarin da ya zama matsala ga 'yancin kasar Sin wajen zabin hanyar warware wannan sabani da kanta, ta kuma shafi yarjejeniyar teku ta MDD da mambobin kasashe 30 suka kulla, wacce ta nuna cewa, kasashen da suka kulla yarjejeniyar suna da 'yancin zabin hanyar warware sabanin da abin ya shafa da kansu.

Bayanin ya ce, a ranar 22 ga watan Janairu na shekarar 2013, Philippines ta yi shiru kan rashin amincewar Sin, ta gabatar da sanarwar yanke hukunci kan neman ikon kulawa da yankin teku tsakaninta da Sin a tekun kudancin kasar Sin. A ranar 19 ga watan Faburairu na shekarar 2013, gwamnatin Sin ta mayar da wannan sanarwa ga hannun Philippines. Daga bisani, sau da dama gwamnatin Sin ta shelanta cewa, Sin ba za ta karba da halalcin batun yanke hukunci da Philippines take yi ba. Amma abin takaici shi ne, a ranar 29 ga watan Oktoban bara, bisa bukatar Philippines, hukumar yanke hukunci ta fidda sakamakon hukunci da ta yanke kan ikon kulawa da yankin teku da sauran batutuwa, inda ta bayyana cewa, Philippines tana da ikon kulawa da yankin tekun.

Bayanin ya ce, ta la'akari da hukuncin da ta yi da kuma ayyukan da ta yi a cikin shekaru 3 da suka gabata, hukuncin da kotun yanke hukunci ta yanke ya karya yarjejeniyar dokar teku ta MDD da kuma sauran dokokin duniya, kuma bai dace da ka'idar kawar da sabani ta hanyar siyasa da yarjejeniyar ta kayyade ba, shi ya sa, ba shi da adalci da daidaici. Abin da kotun yanke hukunci ta yi ya bayyana cewa, Sin ta ki amincewa da hukuncin da kasar Philippines ta yanke da bai dace da dokar duniya ba, ta kuma kaucewa wannan hukunci maras adalci da aka yanke mata. Hukunci maras adalci da kotun ta yanke ya shafi fannoni 4. Na farko, kotun ta habaka ikonta, ta kuma lalata tsarin daidaita rikici da aka kayyade cikin yarjejeniyar, hakan ya kawo cikas ga ikon zabin hanyar kawar da sabani da kasashen suke da su. Na biyu, kotun ta yi kuskure wajen gudanar da ayyukan bincike da yin amfani da dokoki. Na uku, kotun ba ta kawar da sabani ta hanyar siyasa ba, ta kara ruruta sabanin, kuma ta kawo cikas ga zaman lafiya a yankin tekun kudancin Sin. Na hudu, hanyoyin gudanar da ayyukan kotu da kuma tsarin kotun ba su cancanta ba.

Bayanin ya kara da cewa, kasar Sin muhimmiyar kasa ce a duniya, kuma kasa ce da ta ba da gudummawa wajen kafa tsarin dokokin duniya bisa kundin tsarin mulkin MDD. Sin tana girmama ko wace kasa dake daidaita matsaloli ta hanyar da ta zaba da kanta bisa babban tushen yin shawarwari da juna. A matsayin kasar da ta daddale yarjejeniyar, Sin ta ba da babban taimako wajen gudanar da ita, tare da aiwatar da ita yadda ya kamata. Wannan batun yanke hukunci da aka yi bisa bukatar Philippines ya zama wani abin yin wasa da dokoki. Wata hukumar da aka kafa ba tare da samun izni ba, ba za ta gabatar da sakamako mai amfani ba, kuma ba za ta yi tasiri ga ikon da moriyar Sin na mallakar tekun kudancin kasar ba. (Maryam/Lami/Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China