in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe ya jaddada muhimmacin yi wa MDD garambawul
2016-02-11 12:49:34 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sake jaddada wa a ranar Laraba cewa Afrika na iya janye kafa daga MDD idan wannan kungiyar kasa da kasa ta cigaba da kin amincewa nafiyar Afrika samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD. A gaban daruruwan magoya bayan jam'iyyarsa da suka taru domin taya murna kan nasarar wa'adinsa na shugabancin kungiyar tarayyar Afrika a shekarar 2015, mista Mugabe ya bayyana cewa Afrika ta gaji da yadda ake daukarta a matsayin wata saniyar ware a cikin wannan kungiya ta duniya. "Na gayi cikin jawabina na shugaba mai barin gado na kungiyar tarayyar Afrika (AU) a cikin watan Janairu cewa lokaci ya yi gare mu domin mu shaida wa fararen fata cewa muna iya janye wa kuma mu kafa wata kungiya ta daban," in ji shugaban Robert Mubabe. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China