Mr. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Jumma'a a birnin Munich na kasar Jamus, yayin zantawarsa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Reuters.
Ya ce a zahiri take cewa Amurka na shawarta jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami a kasar Koriya ta kudu, sai dai daukar wannan matakin zai shallake bukatar tsaro a zirin na Koriya, ya kuwa shafi fadin wasu sassan yankunan nahiyar Asiya.
Ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya kara da cewa, matakin da Amurka ke aniyar dauka, zai shafi manufofin tsaron kasar Sin, da ma na wasu sauran kasashen nahiyar, don haka Sin ke fatan dakatar da daukar sa.
Mr. Wang ya ce ko da yake ana iya bayyana wasu dalilai na zahiri game da shawarar ta Amurka, a hannu guda kowa ya san manufar hakan ta zarce wadda ake bayyanawa duniya. Hasali ma dai mataki ne da ka iya zama barazana ga tsaron kasar Sin. Don haka ya dace a dakatar da daukar sa ba tare da wani bata lokaci ba. (Saminu Alhassan)