in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta karbi bakuncin dandalin tattalin arzikin duniya kan Afrika na shekarar 2017
2016-05-14 12:02:34 cri
Kasar Afrika ta Kudu ta kasance kasar da aka zaba domin karbar bakuncin dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) kan Afrika na shekarar 2017, in ji ministan kudin Afrika ta Kudu, Pravin Gordhan a ranar Jumma'a.

Afrika ta Kudu na farin ciki matuka na karbar taron koli kan harkokin tattalin arziki a Afrika, in ji ministan kudin Afrika ta Kudu, a yayin da ya halarci taron WEF kan Afrika na shekarar 2016, da aka kammala a birnin Kigali na kasar Rwanda.

Birnin da zai karbi wannan babban taro za a gabatar da shi ba da jimawa ba, in ji mista Gordhan. "Za mu fara kimanta kan mu, domin nuna burin mu na cewa ci gaban Afrika ba wai mafarki ba ne, dake daukar tushensa daga doron kasar Afrika", in ji ministan Afrika ta Kudu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China