in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya ba za'a takaita zirga-zirga ba a yankin arewa maso gabashin kasar
2016-07-05 10:15:56 cri
Mahukunta a Najeriya sun tabbatar da cewar ba za'a takaita zirga zirgar jama'a ba a lokutan gudanar da bukukuwan karamar sallah a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Kashim Shettima shi ne gwamnan jihar Borno, ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala taron gaggawa da ya gudanar da majalisar tsaron jihar a Maiduguri, fadar mulkin jihar.

Gwamnan ya shedawa manema labarai cewar, bayan doguwar tattaunawa da majalisar tsaro ta jihar, da kuma binciken yanayin tsaron da aka gudanar ta jiragen sama da na kasa a Maiduguri, sun amince ba za'a takaita zirga zirgar jama'a da ababan hawa ba a lokutan gudanar da bukukuwan karamar sallar wannan shekara a jihar.

Ya ce gwamnati ta yanke shawarar kyale mutane su gudanar da harkokinsu na bukukuwan sallar ba tare da takaita zirga zirga ba.

Shettima, ya ce gwamnatin za ta ci gaba da tsauraran tsaro a masallatan Idi a fadin jihar, sannan ya bukaci jama'a da su sanar da jami'an tsaro duk wata bakuwar fuska da ba su amince da ita ba.

Wannan shi ne karon farko da jama'a za su gudanar da bukukuwan sallar Idi cikin nutsuwa a shekaru 6 da suka wuce, tun bayan kaddamar da hare haren Boko Haram. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China