in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bukaci a murkushe yan ta'adda da 'yan tada kayar baya a kasar
2016-06-30 11:31:29 cri
A jiya Laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci a kara kaimi wajen dakile kalubalen tsaro dake addabar kasar a halin yanzu.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da cibiyar kwararru ta sojojin kasar a Abuja, Buhari ya nuna goyon bayansa ga sojojin kasar a kokarinsu na tunkarar kalubalen tsaro da ya addabi kasar, wadanda suka hada da hare haren ta'addanci da na kungiyoyi masu dauke da makamai.

Shugaban kasar wanda ministan tsaron kasar birgediya janar Mansur Dan-Ali, ya wakilce shi, ya yaba wa irin kokarin da rundunar sojin kasar ke yi wajen magance barazanar tsaro wanda shi ne daya daga cikin muhimman batutuwan da gwamnatin kasar tafi maida hankali kansu.

Sannan ya jaddada aniyar gwamnatin kasar na tallafawa rundunar sojin kasar da kuma samar musu dukkan abubuwan da suke bukata wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Bugu da kari, ya yabawa kokarin dakarun kasar wajen yaki da ta'addanci a shiyyar arewa maso gabashin kasar, kana ya bukace su da su ci gaba da nuna kwazo game da wannan aikin.

Buhari ya ce gwamnatin kasar za ta ci gaba da bunkasa al'amurran hukumomin tsaron kasar, domin cika muradun wannan gwamnati na samar da dawwamammen zaman lafiya a kasar.

Tun da farko, babban hafsan sojin kasar laftanal janar Tukur Buratai ya ce makasundun kafa cibiyar kwararrun shi ne domin samar da hanyoyin habaka ci gaban sojin kasar.

Ya kara da cewar batun kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar da kan iyakokin kasar ya kusa zama tarihi.

Burutai ya ce, dakarun sojin kasar za su hada kai da sauran hukumomin tsaron kasar domin kawo karshen hare-haren kungiyoyi dake ikirarin daukar makamai da 'yan ta'adda a fadin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China