in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta karbi bakuncin bikin makon nuna sabbin nau'in tufafi na Afrika
2016-07-03 12:20:36 cri
A karshen wannan mako ne Najeriya ta karbi bakuncin bikin makon nuna sabbin nau'in tufafi na Afrika na shekarar 2016 wato AFWN, wanda aka gudanar a Legas cibiyar kasuwancin kasar, kana bikin ya samu halartar jama'a masu yawa.

Sama da masu nuna sabbin nau'in tufafi irin na zamani 60 ne wadanda suka fito daga kasashen Afrika dabam dabam suka nuna sabbin kalar tufafin su a bikin na bana, wanda shine bikin nuna tufafi mafi girma da aka taba gudanarwa a Afrika.

Bikin makon nuna sabbin tufafin na bana, wanda shine karo na uku da aka taba gudanarwa, ya haifar da gagarumin sauyi ga kamfanonin samar da sabbin nau'in tufafi na Najeriya da Afrika baki daya.

Lucky Idike na bankin raya masana'antu, daya daga cikin wadanda suka dauki nauyin bikin na bana, yace bankin ya yi hadin gwiwa ne da AFWN kasancewar wani yanayi ne da zai bunkasa cigaban kamfanonin dake saka tufafi a Najeriya.

Ya kara da cewar, bikin nuna sabbin nau'ikan tufafin zai maida hankali ne wajen fito da sabbin fasahohi da dabarun zamani a tsakanin matasan Najeriya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China