Obasanjo ya yi kiran ne a Litinin a lokacin zantawa da shugaban kungiyar raya ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS), Marcel de Souza, a Abeokuta dake kudu maso yammacin kasar Najeriya.
Ya ce lokaci ya yi da kasashen za su fara amfani da kudi na bai baya, domin a cewarsa zai yi matukar habaka ci gaban tattalin arzikin mambobin kungiyar ta ECOWAS.
Ya kara da cewar, samar da kyakkyawan yanayin ci gaban tattalin arziki na ECOWAS zai tallafawa wajen rage matsalolin rashin ayyukan yi a tsakanin matasan wadannan kasashen, zai kuma tabbatar da bunkasuwar kasashen yammacin Afrika baki daya.
Obasanjo ya bukaci mambobi kasashen da su bullo da sabbin hanyoyin ci gaban kasashensu wanda ya zarta na batun zirga zirgar kayayyaki tsakanin kasahen, kana ya gargadi shugabannin kasashen nahiyar ta Afrika da cewar, rashin kulawa da ci gaban matasa wajen samar musu ayyukan yi babbar barazana ce ga zaman lafiyar kasashen. (Ahmad)