in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta dauki niyyar yaki da sarrafa miyagun kwayoyi
2016-06-28 13:34:37 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana a ranar Litinin cewa za ta cigaba da yaki da sarrafa miyagun kwayoyi.

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Mohammad Abdallah, ya bayyana niyyarsa ta yaki da miyagun kwayoyi a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin wani bikin tunawa da ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa da kasa da aka shirya a birnin Lagos.

Mista Abdallah ya jaddada cewa kasar ta dukufa wajen ganin ta sanya idoo kan amfani da ingantun magunguna ta hanyar kara karfinta na magance wannan matsala.

Shugaban NDLEA ya yi kira ga iyayen yara, al'umma da shugabanni da su ci gaba da ilmantar da matasa illolin shan miyagun kwayoyi a ko wane lokaci.

A cewarsa, a shekarar 2013 an kiyasta cewa mutane miliyan 246 a fadin duniya, a cikin mutum guda akwai yara dan shekaru 15 zuwa shekaru 65 da suka taba shan wani maganin da aka haramta.

Jami'in ya bayyana cewa a shekarar 2013, kimanin mutane 187,000 ne suka mutu sanadiyyar ta ammali da miyagun kwayoyi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China