in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dattijan Najeriya ya ce a shirye yake ya sarayar da 'yancinsa
2016-06-28 11:35:11 cri

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki ya fada a jiya Litinin cewar, a shirye yake ya sarayar da 'yancinsa domin dorewar demokaradiyya da zaman lafiyar kasar.

Saraki ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta iske kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, a yayin da yake mai da martini game da shari'ar da ake masa na yin dokokin jabu na zaman majalisar a shekarar 2015.

Wata babbar kotun shari'a a Abuja ta bada belin Saraki, da mataimakinsa Ike Ekweremadu da wasu mutane biyu bisa shari'ar da ake musu na shirya dokar zaman majalisar ta bogi, wanda ta bai wa Saraki da Ekweremadu damar darewa kujerar shugabancin majalisar.

Sai dai ya bayyana shari'ar da ake masa a matsayin bita da kulli ne ake wa shugabancin majalisar, ya kara da cewar hakan babbar barazana ce ga dorewar demokaradiyyar kasar wadda al'ummar Najeriya suka sha wahala wajen kafa ta.

Saraki ya ce shari'ar dake masa da mataimakinsa Ike Ekweremadu, tamkar take dokokin ne daga bangaren majalisar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China