in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta kaddamar da sabon tsarin hada hadar kudaden kasashen waje
2016-06-28 11:14:44 cri
A jiya Litinin gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sabon tsarin musayar kudaden kasashen waje a hukumance.

Babban bankin kasar (CBN) ya sanar da hakan cikin wata sanarwa tada iske kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, a yanzu haka, sabon tsarin zai sakarwa 'yan kasuwar kasar mara ta yadda za su iya sayen kudaden kasashen waje a fadin kasar daidai da yadda kasuwa ta kama.

Gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele, ya bayyana farin cikinsa game da sabon tsarin, inda ya bayyana cewar a halin yanzu yan kasuwar kasar suna da damar warware duk wani batun da ya shafi musayar kudin kasar Naira da kudaden kasashen waje.

A wani bangaren kuma, ana fatan sabon tsarin zai saukakawa 'yan Najeriya wadanda suke fafutukar neman dalar Amurka domin sayo kayayyaki daga kasashen waje, kuma za su iya neman kudaden da kansu domin bunkasa harkokin kasuwancin su.

Gwamnan babban bankin, ya jaddada aniyar CBN wajen tabbatar da ganin sabon tsarin musayar kudaden ya yi nasara, sannan yayi alkawarin sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansa ta wannan fannin.

Najeriya ta sanar da wannan sabon tsari ne makonni biyu da suka wuce, a matsayin wata hanya ta cike gibin da aka samu sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya, lamarin da ke haifar da koma baya ga sha'anin tattalin arzikin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China