in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Togo na fatan kasancewa ginshiki a yammacin Afrika na sabuwar hanyar siliki
2016-05-28 13:26:29 cri
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya bayyana hangen kasarsa na kasancewa wani ginshiki a yammacin Afrika na shirin sabuwar hanyar siliki da kasar Sin ta alkawarta.

Togo na da niyyar kasancewa tushe a yammacin Afrika na shirin sabuwar hanyar siliki da kasar Sin ta alkawarta da kuma yake dogaro kan dangantakar dake tsakanin kasashe ta hanyar gine gine na kasa da na ruwa, in ji shugaban Togo, a cikin wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Lome, a 'yan kwanaki kadan da suka rage ya gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Sin bisa goron gayyatar takwaransa na kasar Sin Xi Jinping.

Ya jaddada cewa zai samu rakiyar manyan 'yan kasuwa kusan talatin, da zasu halarci dandalin tattalin arziki kan kasar Togo.

Faure Gnassingbe ya tunatar a cikin wannan hira, cewa Sin ta dauki niyyar taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi na tattalin arzkin Afrika.

Game da wannan, ya jaddada cewa Togo na da damammaki da dama domin kasancewa kofar shiga ta yammacin Afrika ga abokan hulda ta kowane hali da kuma musammun ma abokan hulda Sinawa.

Faure Gnassingbe ya bayyana cewa a nan gaba, kamar yadda aka yi a shekarun baya, Togo ta nuna fatanta sosai ganin cewa Sin ta karfafa tallafinta ta fuskar gine ginen tattalin arziki musammun ma hanyoyi, layukan dogo, tashoshin ruwa da na jiragen sama.

Wannan shi ne muhimmin mataki da zai taimakawa kasar bunkasa yankin kayayyaki da zasu taimaka wajen karfafa takarar Togo ta fuskar saukaka kasuwanci musammun ma zuwa kasashen duniya, da kuma mayar da kasar wani dandalin kayayyaki ga yammacin Afrika, in ji shugaban.

Mista Gnassingbe na fatan cewa Togo ta kara samun gajiyar taimakon Sin domin bunkasa nomanta, wanda a cewarsa ya kansance bangaren farko dake kawo bunkasuwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China