Da yake hira da gidan talabajin kasar Togo (TVT) a ranar Lahadi, mista Batchassi ya bada wasu shawarwari domin karfafa tsaron jama'a a kasar Togo, bisa tsarin shirin shigar da matasa wajen karfafa tsaron jama'a a kasar Togo.
Wadannan shawarwari suna da nasaba da karfafa karfin 'yan sanda na kusa da jama'a, lamarin da zai taimakawa wajen kusanto jami'an 'yan sanda da al'umma, yawaita rundunonin tsaro, da kuma kara samar da kayayyakin aiki ga jami'an tsaro.
Haha kuma ya bayyana cewa matakin 'yan sanda na kusa da jama'a na cikin tsarin sake gina jami'an tsaro na matakai daban daban, da shugaban kasa Faure Gnassingbe yake maida hankali a kai.
Shirin na baiwa jami'an tsaro wato 'yan sanda da jandarma da suke tare da al'umma ko da yaushe, damar yadda zasu kara kusantar al'umma, domin suka kasance "'yan sanda na al'umma" in ji mista Batchassi.
Ya kara da cewa, idan suna kusa da al'umma musammun ma matasa, wadannan 'yan sanda za su yi saurin samun bayanai a lokacin da tsaro zai fuskanci wata barazana. (Maman Ada)