in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Rasha da Mongoliya sun dauki niyyar kafa sabon yankin tattalin arziki
2016-06-24 11:13:06 cri

Kasashen Sin da Rasha da Mongoliya sun rattaba hannu a ranar Alhamis a birnin Tachkent kan wani shirin ci gaba dake da manufar kafa wani sabon yankin tattalin arziki tsakanin kasashen uku dake makwabtaka da juna, tare da kuma daukar niyyar karfafa cudanya ta fuskar sufuri da dangantakar tattalin arziki a yankunan dake kan iyakoki.

An rattaba hannu kan shirin, bayan wata ganawa tsakanin shugaban Sin Xi Jinping, shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Mongoliya Tsakhiagiin Elbergdorj a Tachkent, babban birnin Uzbekistan, jim kadan kafin bude babban taron shekara shekara na kungiyar dangantakar Shanghai.

Shugaban Sin ya jagoranci ganawar, da ta kasance irin wannan ta uku. Ya yi bibiyar ci gaban da kasashen uku suka samu kan aiwatar da shirinsu na dangantaka ta matsakaicin lokaci, tare da jaddada cewa, an samu sakamako mai gamsarwa a fannoni daban daban kamar kasuwanci, tattalin arziki, musanyar al'umma da al'adu, sufuri, yawon bude ido da wasannin motsa jiki.

Bisa burin kara bunkasa dangantaka tsakanin bangarorin uku, shugaba Xi Jinping ya shawarta cewa, kasashen uku su ci gaba da aiki bisa shirin kasar Sin na yankin tattalin arziki na hanyar siliki, da dabarun ci gaba na Rasha, kuma musammun ma shirinta na layin dogo da zai ratsa nahiyoyi da kuma shirin Mongoliya na hanyar ciyayi.

Xi Jinping ya yi kuma kira ga kasashen uku da su yi iyakacin kokarinsu domin ba da damar aiwatar da shirin ci gaba dake da manufar kafa wannan sabon yankin kasuwanci, har ma da karfafa dangantakarsu ta fuskar ababen more rayuwa na sufura da hadewa, gine ginen tashoshin ruwa, karfin raya masana'antu, da kiyaye muhalli.

A ganin shugaba Putin, Rasha, Sin da Mongoliya makwabtan kwarai ne kuma abokan juna na kwarai, wadanda dangantakarsu take dogaro bisa tushen daidaici, girmama juna da moriyar juna.

A nasa bangare, shugaba Elbegdor ya bayyana cewa, wannan sabon shirin yankin tattalin arziki tsakanin kasashen uku na da muhimmancin gaske, kuma Mongoliya ta shirya domin aiki kafa da kafa tare da kasashen Sin da Rasha domin bunkasa gine ginen sufuri da kuma karfafa huldar kasuwanci a yankunan iyakoki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China