Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Ghana ta fitar, ta bayyana cewa, matakan magance takaddama kan iyakar ruwan kasashen biyu da kuma karfafa tsaron shiyyar, suna daga cikin batutuwan da shugabannin biyu suka tabo a lokacin ganawarsu ta ranar Laraba.
A jawabinsa shugaba Ouattara ya ce, ya yaba da rawar da takwaransa na Ghana ya taka wajen bunkasa sabon hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Shugabannin biyu sun kuma shaidawa taron manema labarai na hadin gwiwa cewa,tattaunawar tasu ta mayar da hankali kan bunkasa harkokin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da kuma bunkasa tsaro a shiyyar.
Shugaba Mahama ya kai ziyarar aiki ta yini biyu kasar Cote d'Ivoire ne bisa gayyatar shugaba Ouattara .
Kasashen Ghana da Cote d'Ivoire sun gabatar da kara a kotun kula da dokokin teku ta duniya dangane da batun shata kan iyaka ta ruwa tsakanain sassan biyu.(Ibrahim)