Guguwar dai ta Rammasun wadda ba a taba ganin irin ta a yankin na kudancin kasar Sin cikin shekaru 40 da suka wuce ba, na tafe da iska mai karfi da ruwa kamar da bakin kwarya, ta kuma kutsa wasu yankuna na lardunan dake kudancin kasar.
Mahukuntan kasar Sin sun ce baya ga wadanda suka rasu, akwai kuma wasu mutane 2 da suka bace sakamakon wannan bala'i.
Alkaluman baya bayan nan dai sun shaida cewa, bala'in guguwar ya ritsa da al'umma fiye da miliyan 5, yayin da guguwar ke ci gaba da barna a wasu karin yankunan dake bakin teku, ciki hadda wadanda ke lardunan Guangdong, Hainan, da kuma jihar Guangxi mai cin gashin kanta.
Yanzu haka, an tabbatar da mutuwar mutane 8, ciki har da jami'ai masu kula da aikin ceto 2 a lardin Hainan, sai kuma sauran mutane 9 daga lardin Guangxi. (Bello Wang)