in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An saki ma'aikatan da aka sace
2016-06-27 10:48:45 cri
Hukumomin Najeriya sun tabbatar a ranar Lahadi cewa, an riga an saki ma'aikata 'yan kasashen waje 5 da 'yan Najeriya 2, wadanda aka sace su a ranar Laraba da ta gabata a jihar Cross River dake kudancin kasar.

Shugaban rundunar 'yan sandan jihar Cross River, mista Jimoh Ozi-Obeh ya ki bayyana ainihin matakin da aka dauka wanda ya sabbaba sako ma'aikatan, sai dai ya gayawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin cewa, an saki wadannan ma'aikata 7 ba tare da lahanta su ba.

Har yanzu ba a bayyana ko lamarin ya shafi biyan kudin fansa kan mutanen da aka tsare kafin a sako su ba.

Ma'aikata 'yan kasashen waje 5 da aka sace sun zo ne daga kasashen Afirka ta Kudu, da Australia, da New Zealand, kuma dukkansu ma'aikatan kamfanin gine gine ne mai suna Machmahon. An kuma sace su ne a kan gadar Edundun dake yankin Akpabuyo na jihar Cross River.

Wannan kamfanin ginin kuwa ya kasance mai kulla kwangilar hadin gwiwa tare da kamfanin Lafarge Holcim mai samar da siminti dake birnin Calabar, hedkwatar jihar Cross River. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China