Cikin wata sanarwar da ta fitar, shugabar hukumar zartaswar kungiyar uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta jinjinawa shugaban kasar Salva Kiir Mayardit, da gwamnatin sa, bisa goyon bayan da suka baiwa shirin komawar Mr. Machar.
Uwargida Zuma, ta yi fatan cewa wannan mataki zai karfafa burin da ake da shi na kafauwar gwamnatin rikon kwaryar kasar ba tare da wani bata lokaci ba. Kaza lika ta taya al'ummar Sudan ta Kudu murna bisa aiwatar da wannan yarjejeniya, wadda ake sa ran za ta kawo karshen rashin jituwa tsakanin sassan kasar, tare da kokarin su na ganin jaririyar kasar ta koma bisa turbar ci gaba.
Daga nan sai ta ja hankalin shugaban Kiir da Mr. Machar, da su ci gaba da daukar matakan da suka wajaba, na tabbatar da nasarar da aka sanya gaba. Ta ce kungiyar AU ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen tallafawa Sudan ta Kudu da dukkanin irin tallafin da ya dace, na cimma nasarar farfadowar kasar cikin gaggawa. (Saminu Alhassan)