Takardun wadanda aka fidda su a kwanan nan, bayan da aka yi nazari a kan su an gano cewa jam'iyyar JKS ginshiki ce a yakin da aka gwabza da Japanawa a lokacin yakin duniya na 2.
Sojojin Amurka ne dai suka rubuta wadannan takardu, kuma a cikin shekaru 70 da suka gabata, an boye su a ofishin hukumar adana takardun tarihi ta Amurka, da dai sauran wurare, kafin a fidda su duka a 'yan kwanakin baya.
Darektan cibiyar shehun malami Lv Tonglin, ya jagoranci kwararru na kasashen Sin da Amurka wajen nazarin wadannan takardu.
Game da binciken, Shehu malami Lv Tonglin ya ce wadannan takardu sun shaida cewa JKS ta jagoranci al'ummur kasar Sin wajen himmatuwa ga yaki da maharan kasar Japan a lokacin da ake cikin mawuyacin hali. (Bako)