A yayin taron, an tsai da kudurin kaddamar da cikakken zama karo na biyar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 18 daga ran 26 zuwa 29 ga watan Oktoban a nan birnin Beijing.
Bugu da kari, mambobin hukumar siyasa ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun saurari rahoto game da ra'ayoyin da jama'a suka gabatar kan shirin shekaru biyar-biyar na 13 na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, inda suka tsai da kudurin cewa, za a yi wa shirin gyaran fuska bisa ra'ayoyin da jama'a suka gabatar, za kuma a gabatar tare da tattaunawa a kansa a yayin cikakken zama karo na 5 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 18. (Sanusi Chen)