in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan bindiga sun jikkata wasu a lokacin da suke kallon kwallo a Ghana
2016-05-30 13:43:31 cri
Rahotanni daga kasar Ghana na cewa, wasu 'yan bindiga sun harbe wani mutum har lahira kana wasu 16 suka jikkata a unguwar Kabafa da ke kusa da Tamale kimanin kilomta 753 arewa da Accra,babban birnin kasar.

Lamarin dai ya faru ne lokacin da wasu 'yan bingida suka farma wata unguwa a lokacin da aka dauke wutar lantarki sannan suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Wasu dake kallon wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da ake nunawa a ranar Asabar da dare, suna daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Koda ya ke babu wani bayani game da abin da ya haddasa lamari, amma wasu mazauna yankin sun bayyana cewa, hakan ba zai rasa nasaba da rikicin sarautar gargajiya tsakanin al'ummomin Kafarba da Kalampor dake zaune a yankin ba.

Rahotanni na cewa, an turo 'yan bindigan ne domin su sace Kafabarwura Yahaya, mutumin da ya ke ikirarin cewa,shi ne sarkin gargajiya na yankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China