Kakakin rudunar sojan Najeriya Kanar Sani Usman, ya bayyana haka ne cikin wata sanarwarsa, inda ya ce, sojojin runduna ta 21 da hadin gwiwar matasa 'yan sa kai sun kaddamar da simame kan kauyuka fiye da 10, inda suka hallaka 'yan Boko Haram 6 gami da raunata wasu da dama.
Ban da haka kuma, bisa matakan da suka dauka, sojojin gwamnati sun kwato motoci 5 da kekunan hawa 5 daga hannun 'yan Boko Haram, in ji kakakin.
Tun bayan da mayakan kungiyar Boko Haram suka fara tada zaune-tsaye a shekarar 2009, hare haren da suka kaddamar sun haddasa hasarar rayukan mutane fiye da 10,000, musamman ma a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Sojojin Najeriya da jami'an tsaro a matakai daban daban na kasar sun bayyana samun nasarori a kokarin su na murkushe dakarun kunigyar Boko Haram cikin shekarar da ta wuce, inda suka kwaci yawancin yankunan da kungiyar ta taba karbe ikon su a baya.(Bello Wang)