in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi tir da harin ta'addanci da aka kai wa sojojin kasar Sin masu aikin wanzar da zaman lafiya a Mali
2016-06-02 21:24:52 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Mr. Wang Yi, wanda ke ziyarar aiki a kasar Canada, ya gabatar da wani jawabi game da harin ta'addanci da aka kai wa sojojin kasar Sin, wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali.

Mr. Wang Yi wanda ya bayyana hakan a birnin Ottawa a jiya Laraba, ya soki wannan ta'asa da kakkausan harshe. Ya ce muna tir da mummunan matakin kai hari kan ma'aikatan tabbatar da zaman lafiya na MDD.

Kaza lika Mr. Wang ya ce mahukuntan Sin ya bukatar bangarorin da abin ya shafa, su gaggauta daukar matakan binciken lamarin gaba daya, a kuma yanke hukunci bisa doka kan wadanda suka aikata hakan.

Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin ba za ta sauya alkawarinta, na ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duk fadin duniya, ciki har da kasashen Afirka ba. Kuma ba za ta rage kokarinta na taimakawa kasashen Afirka wajen cimma burinsu, na wanzar da zaman lafiya da tsaro a Afirka ba. Bugu da kari, kasar ta Sin za ta ci gaba da shiga aikin tabbatar da zaman lafiya na MDD, da kuma kara nuna goyon baya ga MDD wajen ci gaba da taka muhimmiyar rawa, ta daidaita harkokin kasa da kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China