in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NPFL: Pillars ta lashe Abia Warriors, yayin da Wikki ta ci tura
2016-06-29 10:33:43 cri
Bari mu duba yanayin da ake ciki a tsarin gasar NPFL, wato ta kwararrun kulflikan kwallon kafan kasar Najeriya.

Kulob din Kano Pillars ta sheda niyyarta ta neman zama zakaran tsarin gasar bisa nasarar da ta samu kan Abia Warriors a ranar Lahadi da ta gabata, inda Kano Pillars ta lashe Abia Warriors da ci 5 da ba ko daya a wasan da ya gudana a filin wasan Sani Abacha dake birnin Kano.

Rabiu Ali shi ne na farko da ya fara buga kwallon cikin raga, wanda ya zara kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida mintuna 10 da fara wasan. Daga bisani Razak Adegbite da bai dade da kulla kwantiragi tare da Kano Pillars ba, ya kara buga kwallo daya cikin ragar Warriors, duk da cewa wannan shi ne wasa na farko da ya shiga a matsayin dan wasan Pillars.

Sa'an nan, 'yan wasan Pillars su Bala Zakka, Rabiu Ali, wanda ya sake cin wata kwallo, da Nafiu Kabuga, sun bayar da tasu gudunmawar, ta yadda suka mayar da kungiyar Warriors ba tare da samun damar cin ko da kwallo guda ba.

A nata bangare, kulob din Wikki Tourists dake kan gaba a teburin gasar NPFL, ta gamu da hasara a karon farko bayan da ta ci nasara a wasanni 5 a jere, inda kungiyar Plateau United ta doke Tourists da ci 2 da ba ko daya, a wasan da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata, a filin wasa na Rwang Pam Stadium.

Sai dai har yanzu kulob din Wikki Tourists daga birnin Bauchi tana kan gaba da maki 41, wanda ya fi zarta na Enugu Rangers da ke matsayi na biyu, da maki 2.

Su kuwa 'yan wasan kungiyar Plateau United, Daddy Francis da Anayo Ogbonna, sun bada gudunmawa wajen lashe wasan da kungiyarsu ta yi a karshe, wanda ya zama nasara ta 2 da kungiyar dake birnin Jos ta samu cikin wasanni 11 da ta shiga.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China