Kafin haka babban kocin kungiyar Samson Siasia ya riga ya tabbatar da 'yan wasa 35 ne za su halarci Rio Olympics a watan Augusta. Haka kuma ana saran ganin daga cikin wadannan 'yan wasan, galibin wadanda ke taka leda a kasashen waje za su koma sansanin horaswa da kungiyar ta kafa a Atlanta na kasar Amurka.
Sai dai a nata bangaren, kulob din Manchester City ta ce ba zata yarda da dan wasan gabanta Kelechi Iheanacho, ya halaci wasannin Olympics na wannan karo ba, duk da cewar hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafan Najeriya NFF ta riga ta sanya sunan dan wasan mai shekaru 18 a duniya cikin jerin sunayen 'yan wasa 35 da za su shiga wasannin Olympics.
Kafafen yada labaru na kasar Birtaniya sun bayyana cewa, kulob din Manchester City na son sanya Iheanacho da sauran 'yan wasan kulob din zama tare da sabon kocin Pep Guardiola duk tsawon watanni kafin a fara wani sabon kakar wasanni, don haka ba zai yiwu ba ta bar dan wasan Najeriya ya tafi Brazil a wani lokacin da ake dab da fara wasannin Premier League.
Sai dai an ce niyyar da Man. City ta tsayar ba ta karya doka ba, ganin kulob na da ikon hana 'yan wasanta zuwa halartar sauran wasanni, idan har ta ga babu damar yin hakan.(Bello Wang)