Yayin da suke hira da manema labaru, bayan da aka sanar da sakamakon canki-cankan da aka gudanar don kasa kungiyoyin zuwa rukunai daban daban, kociya da 'yan wasan kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su kamar haka:
"Babu shakka an sanya mu cikin wani rukuni mai wuyar gaske, amma za mu sadaukar da kanmu, da tsayawa kan niyyarmu, Super Eagles za ta iya tsallake shingayen dake gabanta, ta yadda za ta samu damar halartar gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018." in ji mukaddshin babban kocin kungiyar, mista Salisu Yusuf.
A nasa bangaren, Ogenyi Onazi ya ce, " abin da ake bukatar gudanarwa shi ne gabatar da wani shiri nan take. Dole ne mu samu wani koci na mu, farar fata ko kuma bakar fata, wanda za a ba shi muhalli mai kyau don ya gudanar da aikinsa. ' A cewarsa, za a yi iyakacin kokari don samun nasara a kowane wasan da za a shiga, ko a gida ne, ko kuma a kasashen waje.
Ban da haka kuma, shi ma Ahmed Musa ya ce, " Wannan wani rukuni ne mai kyau matuka. Sa'an nan abin da zan iya fada a yanzu shi ne, za mu yi iyakacin kokari don samun damar ficewa daga rukunin da muke ciki."(Bello Wang)