160630-spain-ta-sha-kashi-a-euro-2016-bello.m4a
|
Iceland, wacce ita ce kasa mafi kankanta data taba shiga manyan wasanni, zata cigaba da taka leda a gasar wasannin ta EURO 2016, kuma zata tunkari Faransa a wasannin zagayen kungiyoyi 8.
An yi waje da Ingila, koda yake ta kasance itace ke kan gaba wasu mintuna 4 bayan da aka kaddamar da wasan, bayan da captain Wayne Rooney yayi bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Amma Iceland ta yi nasarar zara kwallayenta ne mintuna biyu baya. Kari Arnason yayi nasarar kade kwallayen da aka sha kai farmaki gidansu Ragnar Sigurdsson.
Duk da cewar Ingila ta yi ta kokarin tsare gida, amma Iceland tayi nasara da ci 2-1 a yayin da ya rage mintuna 18 daga harin farko mai muhimmanci da suka kai. Dan wasan bayansu Kolbeinn Sigthorsson ya buga kwallon gida sannan mai tsaron ragar Ingilan Joe Hart ya buge kwallon da hannunsa na hagu, amma duk da hakan bai hana kwallon fadawa cikin ragarsu ba.
Roy Hodgson ya bada sanarwar yin murabus daga aiki a matsayin manajan kungiyar wasan Ingila, bayan da suka sha kashi da ci 2-1 a hannun Iceland.
Hodgson ya fada a taron manema labaru cewar ya ji matukar takaici game da sakamakon wasan da suka buga, yace sam 'yan wasan basu yi wani abin azo a gani ba a bisa yadda yayi tsammani, kuma hakan sam ba abinda za'a amince dashi bane.
A filin wasan na Saint-Denis, Italy ta yi kokarin kare kanta don tabbatar da niyyarta ta kwace kofin daga hannun Spain domin kafa tarihi, da ci 2-0.(Ahmad Fagam)