in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Messi yayi murabus daga wasan kwallon kafa na kasa da kasa
2016-06-29 10:30:31 cri
Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wa kungiyar kasarsa wato Argentina wasa a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da kungiyar wasa ta Chile ta doke Argentina a wasan karshe na gasar cin kofin Copa America.

A yayin da yake hira da manema labaru bayan kammala wasan, shahararren dan wasan ya ce, ya riga ya kammala aikinsa a kungiyar wasan Argentina, kuma a wannan karo ya yi iyakar kokarinsa amma duk da haka ba su samu damar zama zakara ba, hakan ya sa yake bakin ciki matuka, in ji dan wasan na kulob din Barcelona mai shekaru 29 a duniya.

Hakan ya kasance shekaru 2 ke nan a jere da Chile take samun damar lashe Argentina a wasannin karshe ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda ta lashe Argentina da ci 4 da 2. Kuma da wannan wasan aka kawo kashen gasar cin kofin Copa America ta wannan karo wanda aka gudanar da ita a kasar Amurka don murnar cika shekaru 100 da kaddamar da gasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China