Cikin sanarwar shugaban kamfanin Suning mista Zhang Jindong, ya ce yana alfahari da hadin gwiwar da aka kulla tare da Inter Milan, wanda yake da dogon tarihi da nasarori sosai a fannin wasan kwallon kafa. Bisa wannan mataki, a cewar mista Zhang, Suning zai taka muhimmiyar rawa a harkar wasannin motsa jiki, wadda za ta kasance daya daga cikin ginshikin tattalin arzikin kasar Sin bayan shekaru 5 masu zuwa.
Dama dai tun daga karshen shekarar bara, Suning ya riga ya sayi wani kulob din wasan kwallon kafa a nan kasar Sin, wanda ya lakaba masa Suna Suning FC. Daga bisani kamfanin ya kashe kudin Euro fiye da miliyan 100 don sayo wasu fitattun 'yan wasa kamarsu Alex Texeira, da tsohon dan wasan tsakiyar Chelsea Ramires.
An ce ta hanyar sayen hannayen jarin Inter Milan, Suning zai samu damar kyautata tsarin kula da kulob din sa, da tsarin horar da 'yan wasa, da dai sauransu. Kamar yadda babban kocin kungiyar Suning FC Gong Lei ya fada. Ya ce za a kai matasa 'yan kwallo 100 zuwa Italiya a kowace shekara, don samun horo a makarantar horar da matasa ta Inter Milan. Hakan zai taimakawa raya harkar wasan kwallon kafa a kasar Sin, a cewar mista Gong.(Bello Wang)