160609-ana-tunawa-da-muhammad-ali-a-matsayin-abokin-kasar-sin-bello.m4a
|
Fitaccen dan wasan, wanda ya taba lashe lambar zinare a wasannin Olympics na shekarar 1960, kuma ya kasance zakaran damben duniya har karo 3, ya taba ziyarar kasar Sin a shekarar 1979, inda ya samu damar ganawa da mataimakin firaministan kasar na wancan lokaci marigayi Deng Xiaoping, jami'in da ya gabatar da manufar gyare-gyare da bude kofa a nan kasar Sin.
A lokacin ganawarsu, mista Deng ya fada wa Muhammad Ali cewa, Sin na daukar sa a matsayin amini, don haka kasar na masa marhabin. Haka kuma wasan dambe zai iya zama wata hanya ta kara fahimtar juna, da kulla dankon zumunta tsakanin Sinawa da Amurakawa, in ji shi Mr. Deng.
Ali ya sake zuwa kasar Sin a shekarar 1985. A lokacin, duk inda ya shiga, Sinawa sun rika yi masa tarba hannu biyu biyu. Sa'an nan taken sa na "tsalle kamar malam-buda-mana-littafi, kana harbi kamar kudan zuma" ya shahara a nan kasar Sin, yayin da al'ummar kasar ke kallonsa a matsayin abin koyi, musamman a zukatan matasa masu neman zama fitattun 'yan wasa.
A nasu bangaren, wasu shahararrun 'yan wasan dambe na kasar Sin sun nuna juyayi kan rasuwa Muhammad Ali. Xiong Chaozhong, wanda ya kasance zakaran dambe a tsarin gasar WBC, ya ce bayan da ya samu kambinsa a shekarar 2012, uwargidan Ali Madam Lonnie ta gana da shi. Inda ya bayyana masa cewa Ali ya amince ya horas da shi fasahar dambe, saboda ya taba yiwa tsohon firaministan kasar Sin Deng Xiaoping alkawarin cewa, idan har wani Basine ya zama zakarar damben duniya, zai dauki nauyin horar da shi da kansa.
A nasa bangare Zou Shiming, wanda ya ci lambobin zinariya guda 2 a wasannin Olympics a fannin wasan dambe, ya ce, Muhammad Ali ya ba shi kwarin gwiwa sosai, duba da kwarewarsa ta fuskar wasan dambe, da yadda ya yi yaki da nuna bambanci tsakanin al'umma, musamman ma tsakanin bakake da fararen fata.(Bello Wang)