in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Olympics ya sanar da kafa kungiyar 'yan gudun hijira da za ta halarci Olympics a Rio
2016-06-08 09:09:01 cri
Wasu 'yan gudun hijira 10 za su halarci wasannin Olympics da za su gudana a birnin Rio na kasar Brazil a watan Agusta. 'Yan wasan za su daga wata sabuwar tuta a madadin dukkan 'yan wasan da suka yi gudun hijira, sakamakon tashe tashen hankula dake aukuwa a kasashe da yankunan su.

Tawagar dai za ta kunshi 'yan wasan tsere 5 daga kasar Sudan ta Kudu, da 'yan wasan ninkaya 2 daga Syria, da 'yan wasan judo 2 daga jamhuriya Dimokuradiyar Congo, gami da wani dan wasan gudun ya-da-kanen-wani na kasar Habasha.

Wadannan 'yan wasa da wasu jami'ai aka hada a tawagar 'yan gudun hijirar, su ne na farko a duniya, an kuma kafa tawagar ne da nufin karfafa wa 'yan gudun hijirar kasashe daban daban gwiwa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China