--A jiya ne a ka kai ruwa rana tsakanin sojoji da 'yan sanda a gidan gwamnatin jihar Borno da ke garin Maiduguri,a lokacin da ake rabawa 'yan gudun hijira shinkafa, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar dan sanda daya da wasu fafaren hula da ke jiran nasu kason.(Daily Trust)
--Dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya Samuel Ikon daya daga cikin 'yan majalisun wakilan kasar uku da ake zargi da neman karuwai a lokacin da suka ziyarci kasar Amurka, ya rubutawa jakadan Amurka a Najeriya James Entwiste wasika, inda ya yi barazanar neman a wanke shi daga zargin da aka yi masa a dukkan kotunan Najeriya da kuma Amurka.
Dan majilsar ya bayyana a cikin wasikar da ya rubutawa jakadan cewa, ba shi da lafiya a lokacin ziyarar, sannan bai yi jima'i da kowa ba, saboda ba shi da lafiya.(Vanguard)