in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Najeriya an damke mai samarwa Boko Haram makamai
2016-06-14 10:10:00 cri

Mahukunta a tarayyar Najeriya sun tabbatar da cewa, jami'an tsaron kasar sun yi nasarar cafke wani jigo a kungiyar Boko Haram wanda ake zargin shi ne wanda ke samar wa kungiyar makamai da abubuwa masu fashewa a yankin arewa maso gabashin kasar.

Ibrahim Abdullahi, kwamandan hukumar tsaron al'umma wato NSCDC na jahar Borno ya sheda wa 'yan jaridu a Lahadin da ta gabata cewa, an kame madugun na Boko Haram ne a yankin Askira Uba lokacin wani samame da jami'an tsaron ke gudanarwa a yankin.

Ana zargin mutumin da laifukan da suka hada da daukar mutane aiki don shigar da su kungiyar, da samar da makamai da kuma ababan fashewa ga kungiyar ta Boko Haram, kuma tuni aka mika shi hannun sojoji domin ci gaba da bincike.

A cewar Abdullahi, tuni mutumin ya amince da laifin da ake tuhumarsa, har ma ya tabbatar da cewa, ya shigar da 'ya'yansa uku cikin kungiyar ta Boko Haram.

A 'yan kwanakin nan, dakarun Najeriyar na samun galaba a yakin da suke da kungiyar Boko Haram, har ma sun yi nasarar kwato dukkan yankunan da kungiyar take rike da ikonsu a lokutan baya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China