Kakakin rundunar sojojin Najeriya kanar Sani Usman wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin Lagos cibiyar kasuwancin kasar, ya ce, sojojin sun yi nasarar kashe tare da lalata maboyar 'yan ta'addan da dama. Baya ga makamai da albarusai da sauran kayan fada da sojojin suka kwatao a lokacin da suke kadamar da hare-hare kan mayakan na Boko Haram a jihar Borno kadai.
Kanar Sani ya ce, dakarun bataliya ta musamman ta 7 ta samu wannan nasara ce tare da taimakon hari ta sama daga mayakan saman kasar.,
Kakakin ya kara da cewa, sojojin sun kaddamar da hare-hare da sanyin safiyar jiya ne da nufin kawar da gyauron mayakan Boko Haram daga cikin sansanoninsu a kauyuka da dama na karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.
Kanar Usman ya kuma bayyana cewa, an garzaya da mata da yaran da aka ceto daga hannun mayakn Boko Haram zuwa sansanonin 'yan gudun hijira daban-daban da ke jihar bayan da aka kammala tanance su.(Ibrahim)