in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta karbe ikon garin Bosso
2016-06-07 09:33:00 cri

Wasu rahotanni na cewa, mayakan Boko Haram sun karbe iko da garin Bosso dake jamhuriyar Nijar, bayan wani bata kashi tsakaninsu da dakarun sojojin Najeriya da Nijar.

Wata majiya ta ce, mayakan na Boko Haram sun amshe ikon garin na Bosso dake kan iyakar Nijar da Najeriya ne a daren ranar Lahadi, yini uku bayan da suka gwabza kazamin fada da sojojin kasashen biyu a ranar Jumma'a.

Ko da a ranar Jumma'ar ma dai sai da mayakan na Boko Haram suka hallaka sojojin kasashen biyu su 30, kana wasu 70 suka jikkata, lamarin da ya tilasawa sojojin ja da baya, daga bisani kuma harin ranar Lahadi ya sanya mayakan Boko Haram din amshe garin baki daya.

Mayakan Boko Haram dai sun hallaka mutane sama da 10,000, tare da tilasawa dubban al'ummu, musamman ma wadanda ke arewa maso gabashin Najeriya kauracewa gidajensu tun fara kaddamar da hare-harensu a shekarar 2009. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China