Mr. Li ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi amana ga hulda da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Jamus. Kasar Sin tana maraba da kamfanonin kasar Jamus da na sauran kasashen duniya wajen zuba jari a kasarta. Sannan yana fatan kasashen Sin da Jamus za su karfafa hadin gwiwarsu da kara yin musayar ra'ayi a kungiyar G20, da kuma dukufa kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya tare, domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
A nata bangaren, Angela Merkel ta bayyana cewa, huldar dake tsakanin kasashen Jamus da Sin tana samun bunkasuwa sosai. A matsayin wani muhimmin tsari, taron musayar ra'ayi a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu ya ingiza bunkasuwar hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu a dukkan fannoni. Kasar Jamus tana son tabbatar da "shirin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Jamus" da kasashen biyu suka tsara a gun taron musayar ra'ayi a tsakaninsu karo na 3 tare da kasar Sin, da kuma kiran taron musayar ra'ayi karo na 4 yadda ya kamata, domin inganta hulda da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.(Lami)