Yanzu haka dai an kammala aikin kyautata gine-ginen wuraren karbar taron kolin, da wuraren da shugabannin za su zauna, da ragowar sauran wurare, ana kuma shiga matakan karshe na kyautata yanayi a wurin.
Sakataren gwamnatin birnin Hangzhou Zhao Yide, ya ce yana fatan amfani da wannan taro, don sanarwa duniya yanayin da kasar Sin ke ciki, da nasarorin da Sin ta samu ta hanyar gudanar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kana da zamanintar da kasar, da halayyen Sinawa.
Ya zuwa yanzu, an kusan kammala dukkanin ayyukan sharen fagen, nan gaba kuma za a ci gaba da ba da tabbaci don gudanar da wasu hidimomi, don tabbatar da gudanar taron cikin nasara.(Bako)